1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Iran ta yi watsi da duk wani yunkuri na tattaunawa da Amirka game da shirye-shiryenta na mallakar makaman nukiliya.

Bayan da Hukumar Kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa, wato IAEA, ta zartad da kudurin kai karar Iran gaban kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, mahukuntan kasar sun fara daukan tsauraran matakan mai da martani da suka yi barazanar yi tun da farko. Da yake amsa tambayoyin maneman labarai yau a birnin Teheran, kakakin gwamnatin Iran din Gholamhossein Elham, ya ce babu wani sauyi a manufofin kasarsa game da Amirka. Sabili da haka, wani batun farfado da huldodin dangantaka da Washington ko kuma tattaunawa da mahukuntan kasar ma bai taso ba. Kakakin ya kara da cewa, kasashen Yamma sun yi babban kuskure da kai wannan batun ga kwammitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya. Saboda a ganinsa, wannan matakin na nuna adawar da kasaashen Yamman ke yi ne ga ci gaban Iran.

Tun jiya ne dai Iran din ta ce ta katse duk wasu huldodi da kuma ayyukan hadin gwiwa da Hukumar IAEA. Kuma ta kara da cewa, za ta fara sarrafa sinadarin Yureniyum din, ta kuma hana sifetocin hukumar damar shiga gudanad da bincke cikin kafofinta.

Iran dai ta yanke wannan shawarar ne kwana daya, bayan da Hukumar IAEA din ta zartad da kuduri, karkashin angizon Amirka, na kai kararta gaban kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya.