Iran ta yi wasti da barazanar kai mata hari | Labarai | DW | 09.04.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Iran ta yi wasti da barazanar kai mata hari

Kasar Iran ta baiyana rahotanni dake cewa Amurka na shirin kai mata farmaki da cewa soki burutsu ne kawai ake yi domin sanyaya mata gwiwa ta yi watsi da shirin ta na makamashin nukiliya. Kakakin maáikatar harkokin wajen Iran Hamid Reza Asefi yace sun dauki wannan yunkuri a matsayin farfaganda wace ba za ta tasiri ba. Wasu rahotanni biyu na Amurka da aka wallafa a karshen mako sun yi nuni da cewa Amurka na nazarin wasu shawarwari na yiwuwar kai farmaki a kan tashoshin nukiliyar Iran. Gwamnatin Amurka ta George W Bush wadda ke zargin Iran da yunkurin kera makaman nukiliya ta sha nanata cewa tana nazarin matakai da dama wadanda suka hada da sasantawa ta fuskar diplomasiyya domin kawo karshen takadamar cikin ruwan sanyi. A hannu guda kuma sakataren harkokin wajen Britaniya Jack Straw wanda kasar sa ta kulla kawance da Amurka wajen afkawa kasar Iraqi a shekarar 2003 ya yi watsi da shawarar yin amfani da karfin soji a kan Iran. Yace ko da yake basu da hakikanin tabbas a game da manufar Iran, a dangane da shirin ta na nukiliya, amma ba hujja ba ce ta afka mata da karfin soji.