Iran ta yi tir da kalaman shugaba Chirac na Faransa
January 22, 2006Iran ta yi Allah wadai da sanarwar da shugaban Faransa Jacques Chirac ya bayar a tsakiyar makon jiya cewar Faransa na da ´yancin yin amfani da makaman nukiliya a kan kasar da ta kaddamar da ta´addanci a kanta. Wata sanarwa da ma´aikatar harkokin wajen Iran ta bayar ta ce barazanar ta shugaba Chirac ta fito da aniyar kasashen duniya masu mallakar makan nukiliya a fili. Shi ma shugaban bangaren jam´iyar SPD a majalisar dokokin Jamus Peter Struck ya nesanta kanshi daga kalaman na shugaba Chirac. Struck ya ce ba ya tsammanin za´a iya yakar ayyukan ta´addanci da wani harin makamin nukiliya. Gwamnatin Jamus dai ba ta fito karara ta yi Allah wadai da furucin na shugaba Chirac ba. A kuma halin da ake ciki Isra´ila ta sake gargadin Iran game da shirinta na kera makaman nukiliya. Ministan tsaro Shaul Mofaz ya yi tir da kalaman shugaba Mahmud Ahmedi-Nijad na yin kira da a goge Isra´ila daga taswirar duniya.