Iran ta yi maraba da rahoto kan shirinta na nukiliya | Labarai | DW | 04.12.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Iran ta yi maraba da rahoto kan shirinta na nukiliya

Iran ta yi maraba da rahoton hukumar leƙen asiri na Amurka kan shirinta na nukiliya wadda tace gwamnatin Iran tuni ta dakatar da kokarinta na ƙera makaman nukiliya a 2003.Minsitan harkokin wajen Iran Manoucher Mottaqi yace rahoton ya tabbatar da cewa Iran tana shirinta don zaman lafiya ne.Mai bada shawara kan harkokin tsaron kasa na Amurka Steven Hadley yace rahoton ya nuna cewa manufofin gwamnatin Bush akan Iran sunyi anfani.Kodayake ƙwarraru kan harkokin leƙen asiri waɗanda suka shirya wannan rahoto sunce Tehran ta bar hanyoyiyn komawa ƙera makaman a buɗe.Firamninistan kasar Burtaniya Gordon Brown ya ce duk da haka zai ci gaba da ƙara matsin lamba na ganin an laƙabawa Iran takunkumi haka shima Firaministan Israila Ehud Olmert yace zai ci gaba da haɗa kai da Amurka don tabbatar da cewa Iran bata mallaki makaman nukiliya ba.Hakazalika Faransa tayi kira ga manyan ƙasashen duniya da su ci gaba da matsawa Iran duk da wannan rahoto da hukumar leken asirin na Amurka ta fitar.