Iran ta yi kira da a shirya wani taro tsakaninta da wakilan EU | Labarai | DW | 29.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Iran ta yi kira da a shirya wani taro tsakaninta da wakilan EU

Jami´an Iran sun nuna bukatar shirya wani taro da takwarorinsu na Birtaniya Jamus da kuma Faransa da nufin tattaunawa akan shirin nukiliyar kasar da ake fito-na-fito akai. Jami´an KTT sun tabbatar da cewa a gobe litinin za´a yi wani taro da mukaddashin mai shiga tsakanin a tattaunawar nukiliyar kasar wato Javad Vaedi a birnin Vienna. A kuma halin da ake ciki sakatariyar harkokin wajen Amirka Condoleezza Rice tana kan hanyar zuwa birnin London inda a goben idan Allah Ya kaimu ministocin harkokin wajen kasashe 5 masu kujerun dindindin a kwamitin sulhun MDD tare da takwaransu na Jamus zasu tattauna a wani yunkuri na warware wannan rikici. Da farko ministan harkokin wajen Jamus F-W Steinmeier yayi gargadin cewa ana iya sanyawa Iran takunkuman karya mata tattalin arziki idan ta ki cimma yarjejeniya da gamaiyar kasa da kasa.