1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran ta yi kira da a koma kan teburin shawarwari game da shirin ta na nukiliya

November 6, 2005
https://p.dw.com/p/BvMF

Iran ta yi kira ga KTT da su koma kan teburin shawarwari dangane da shirin ta na nukiliya da ake takaddama a kai. Kamar yadda kafofin yada labarun kasar suka nunar, yanzu haka dai gwamnati a birnin Teheran ta aikewa wakilan kungiyar EU a shawarwarin wato Jamus da Faransa da kuma Birtaniya takardun dake kunshe da wannan kira. Bugu da kari gwamnatin Iran ta ba wa sifetocin hukumar dake kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa wato IAEA izinin gudanar da bincike a wani sansanin sojin kasar. Iran dai na shan matsin lamba daga kasashen duniya saboda shirin ta na nukiliya da ake kace-nace a kai. Kasashen yamma musamman Amirka na zargin ta da shirin kera makaman nukiliya a boye. To amma Iran ta ce shirin na ta na lumana ne.