1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran ta yi ikirarin gabatar da shirin makamashin nukiliya ta musamman

February 11, 2012

Hukumar kula da makamashi ta duniya IAEA ta zargi Iran da sarrafa makaman kare dangi, abun da Iran sau da yawa tana karyartawa.

https://p.dw.com/p/1422f
Three hands are seen, the bottom right one of a delegation member, as Iran's President Mahmoud Ahmedinejad gestures during a press conference at the U.N. Climate Conference in Copenhagen Friday Dec. 18, 2009. The largest and most important climate change conference is on its last scheduled day, aiming to secure an agreement on how to protect the world from calamitous global warming. (AP Photo/Peter Dejong)
Shugaba Mahmud Ahmedinejad na IranHoto: AP

Shugaban kasar Iran Mahmoud Ahmedinejad ya sha alwashin kaddamar da wasu shirye-shiyen makamashin nukiliya masu mahimmanci a 'yan kwanaki masu zuwa, ya kuma yi kakkausar suka ga Israila.

A wani jawabin da ya gabatar na tunawa da juyin juya halin Islaman Iran wanda aka gudanar a shekarar 1979, ya ce kasarsa ba zata ba da kai bori ya hau ga irin takunkumin da kasashen yamma ke kakaba mata ba, ko kuma ma irin barazanar daukar matakin soji, da Amurka da Israila ke yi mata.

Jama'a kusan dubu 30 suka taru a dandalin Azadi, da ke babban birnin kasar wato Tehran suna jinjinawa Ahmedinejad yayin da yake wannan jawabi, duk da sanyin hunturun da ake yi.

Ahmedinejad bai bayar da cikakken bayani dangane da wadannan mahimman shirye-shirye da kasar zata kaddamar ba, to sai dai hukumar kula da makamashi ta duniya IAEA ta zargi Iran da sarrafa makaman kare dangi, abun da Iran sau da yawa tana karyartawa. Amurka da kungiyar tarayyar Turai sun yi ta sanyawa Iran takunkumin karya tattalin arziki domin ta yi amfani da karfin tuwo wajen dakatar da shirin makamashin nukiliyar kasar, amma Iran ta yi watsi da wadannan matakan ta kuma ce mafita ga wannan batu ita ce kamanta adalci da kuma mutunta 'yancin da Iran take da shi ta mallaki makamashin nukiliya kana kuma bangarorin su koma kujerar tattaunawa.

Mawallafiya: Pinado Abdu-Waba
Edita: Mohammed Awal Balarabe