Iran ta yi gwajin jirgin yaƙi mai sarrafa kansa | Labarai | DW | 22.08.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Iran ta yi gwajin jirgin yaƙi mai sarrafa kansa

A karon farko Iran ta yi gwajin jirgin yaƙi mai sarrafa kansa ba tare da matuƙi ba.

default

Shugaban Iran Mahmoud Ahmadinejad, ke jawabi a lokacin ƙaddamar da jirgin yaƙi na farko mai sarrafa kansa.

Shugabannin Iran sun ƙaddamar da jirgin yaƙinsu na farko mai sarrafa kansa ba tare da matuƙi ba wanda ke iya cin tazarar kilomita 1000. Shugaban ƙasar Mahmoud Ahmedinejad ya yi jinjina ga wannan cigaba yana mai cewa ya ɗaukaka ƙarfin rundunar sojin ƙasar. Wannan dai ya zo ne kwana guda bayan da ƙasar ta fara ɗura makamashi a murhunta na nukiliya. A martaninta Israila ta ce ba za ta saɓu ba a ƙyale iran ta mallaki makamin Nukiliya, sai dai kuma yawancin ƙasashen yammacin turai na ganin cewa tashar makamashin wanda Rasha ta ginawa Iran ba ta da wata barazana saboda sa ido da kuma hannun gamaiyar ƙasa da ƙasa a wannan aiki.

Mawallafi : Abdullahi Tanko Bala

Edita : Umaru Aliyu