Iran ta yi belin Clotilde Reiss | Siyasa | DW | 17.08.2009
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Iran ta yi belin Clotilde Reiss

Bayan zargin da hukumomin Teheran suka yiwa Clotilde Reiss, na bamɓarar da gwamnati, a yanzu an samu belin ta daga kurkuku

default

Clotilde Reiss ta hito daga kurkukun Iran

Wata sanarwar da Ofishin Jakadancin ƙasar Faransa ya fitar, ya bayyana cewar, Gwamnatin Iran ta bayar da belin wata bafaranshiya - Malamar Makarantar data tsare, bisa zargin tallafawa zanga zangar da 'yan adawa a ƙasar suka yi, bayan zaɓukan shugaban ƙasar da aka yi a ranar sha biyu ga watan Yuni.

Ofishin Shugaban ƙasar Faransa, Nikolas Sarkorzy ya fitar da sanarwar dake bayyana cewar, gwamnatin ƙasar Iran ta bayar da belin wata malamar makaranta - 'yar asalin Faransar data cafke makonni shiddan da suka gabata kuma ta tsareta a wani gidan yarin dake Tehran - babban birnin ƙasar. Sanarwar ta ce a yanzu malamar - mai suna Clotilde Reiss, zata ci gaba da zama a ofishin Jakadancin Faransar ne har ya zuwa lokacin da Kotu zata yanke mata hukunci.

Reiss, wadda 'Yar shekaru ashirin da huɗu ce a duniya, gwamnatin Iran ta zargeta da laifin taimakawa ƙoƙarin hamɓarar da gwamnatin ƙasar, wanda ta ce ƙasashen yammaci suka yi, bayan sanar da zaɓukan shugaban ƙasar da aka yi a ranar sha biyu ga watan Yuni, kana aka cigaba da tsare ta tun a farko farkon watan Yuli.

Hakanan a cikin makon jiya ne, gwamnatin Iran ta saki wata ma'aikaciyar ofishin Jakadancin na Faransa - amma 'yar Iran, Nazak Afshar - itama dai akan beli, kana zata cigaba da zama a Ofishin Jakadancin, ya zuwa lokacin da za'a yanke mata hukunci, bisa zargin taka rawa a jerin gwanon nuna adawa da sakamakon zaɓen.

Bernard Hourcade, ƙwararre ne akan harkokin da suka shafi ƙasar Iran, a wata cibiyar bincike ta ƙasar Faransa - mai suna CNRS; ya yi tsokaci akan sakin da gwamnatin Iran ɗin ta yiwa Matan biyun:

Wannan matakin farkone muka cimma. Belin, na tattare da wasu sharuɗɗa ne. A yanzu muna jiran sakamakon ƙarshe na kotu ne, amma bamu san wace rana bace.

Sai da a yayin da ake jiran ranar, Ofishin Shugaba Sarkozy, ya yi kira ga hukumomin Iran, dasu janye tuhumar da suke yiwa Matan, domin a cewar ofishin, zarge zargen basu da tushe balle makama.

Shi kuwa shugaba Nikolas Sarkozy, godiyarsa ya miƙa ga ƙungiyar tarayyar Turai, da kuma gwamnatin ƙasar Syria, bisa shiga tsakanin da suka yi wajen samun belin matar.

A nashi ɓangaren, mahaifin Clotilde Reiss, wato Remi Reiss, wanda ya zanta da ɗiyar tasa bayan sakinta, bayyana jin daɗinsa ya yi game da wannan cigaban da aka samu:

Munyi farin ciki da aka sassauta zarge zargen da ake yi mata. A yanzu ana tuhumarta da bada haɗin kai wajen haddasa zanga zanga. A taƙaice dai, munyi murna da matakin farkon da aka cimma.

Gwamnatin Iran ta zargi malamar makarantar da laifin leƙen asiri, da kuma shiga cikin zangar da 'yan adawa a Iran suka yi na yin Allah wadai da sakamakon zaɓen da shugaba Mahmud Ahmadinejad ya lashe. Hakanan gwamnatin na tuhumarta da aikewa ofishin Jakadancin rahotanni game da zaɓukan na ranar sha biyu ga watan Yuni. A ranar ɗaya ga watan Yuli ne kuma aka tsare Reiss a filin Jirgin samar birnin Tehran - a lokacin da take shirin ficewa daga ƙasar.

Mawallafi: Saleh Umar Saleh

Edita: Yahouza sadissou