Iran ta yi barazanar janye wa Japan kwangilar da aka ba ta, ta haƙo man fetur a ƙasar. | Labarai | DW | 25.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Iran ta yi barazanar janye wa Japan kwangilar da aka ba ta, ta haƙo man fetur a ƙasar.

Wani babban jami’in hukumar man fetur na ƙasar Iran, ya gargaɗi Japan, da ka da ta yi ta tafiyar hawainiya wajen gudanad da ayyukan kwangilar da aka ba ta, ta gina rijiyoyin haƙo man fetur, a filin nan mai tarin albarkatun mai na Azadegan. Iran ɗin dai na tuhumar Japan ne, da yin tafiyar hawainiya a kan wannan aikin, saboda angizon da Amirka ke yi wa mahukuntan birnin Tokyo, da kiran da take yi wa Japan ɗin na ta dakatad da zuba jari a Iran, saboda manufofin makamshin nukiliyan da Teheran ta sanya a gaba.

A cikin wata fira da ya yi da kafar yaɗa labaran nan ta Kyodo News ta Japan ɗin a birnin Teheran, Mehdi Bazargan, shugaban Hukumar kula da bunƙasa ayyukan man fetur na Iran, ya bayyana cewa, ƙa’idodjin yarjejeniyar da aka cim ma da Japan game da wannan aikin, sun sanya wa’adin kammala shi ne a cikin wwatan Satumba. Idan ko kawo lokacin ba a sami wani muhimmin ci gaba ba, to iran za ta janye kwangilar kai tsaye. Jami’in ya ƙara da cewa, Iran za ta iya juyawa ga Sin ko kuma duk wanda aka samu da zai iya gudanad da aikin.