1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran ta shiga mataki na biyu na fadada shirin sarrafa uranium

October 28, 2006
https://p.dw.com/p/Bue6
A hukumance Iran ta tabbatar da cewa ta inganta aikinta na sarrafa sinadarin uranium inda ta tura iskar gas cikin wasu bututu a mataki na biyu na gwajin karfin karafan uranium da nufin fadada shirinta wanda kasashen yamma ke zargin cewa na kera makaman nukiliya ne. Mataimakin shugaban hukumar makamashin nukiliya na Iran ya ce dukkan matakan biyu na inganta karafan uranium da kimanin kashi 5 cikin 100. A dangane da haka shugaban Amirka GWB ya ce dole gamaiyar kasa da kasa ta karfafa kokarin da take yi na hana Iran samun fasahar nukiliya. To amma ministan tsaron Rasha Sergei Ivanov ya ce ka da a yi riga malama masallaci da cewa Iran na da fasahar samar da ingantaccen sinadarin uranium wanda za´a iya kera makamin nukiliya da shi. Saboda haka shi fa bai ga wani abin damuwa a nan ba.