1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran ta sanad da Hukumar IAEA bisa manufa cewa za ta katse duk wasu ayyukan hadin gwiwa da ita.

February 6, 2006
https://p.dw.com/p/Bv97

A cikn matakan mai da martanin da Iran take dauka dangane da shawarar da Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya ta Kasa da Kasa, wato IAEA a taKaice ta yanke, ta kai Kararta gaban kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, saboda tuhumar da take yi mata ta yunKurin sarrafa makaman nuiliya, mahukuntan Kasar sun ba da sanarwar cewa sun sanad da Hukumar ta IAEA bisa manufa cewa, za su fara cikakken aikin sarrafa sinadarin Yureniyum.

Da yake yi wa maneman labarai jawabi yau a birnin Teheran, shugaban tawagar Kasar mai tattauna batun makamashin nuklilyan, Ali Larijani ya ce nan ba da dadewa ba, za a cire duk hatiman hukumar IAEA din daga kafofin nukilyan Iran a cikin `yan kwanaki masu zuwa nan gaba. Kuma za a yi hakan ne gaban sifetocin binciken makamashin hukumar. Har ila yau dai, Turai da Amirka na bayyana fargabarsu ta cewa Iran za ta yi amfani da kafofin ne wajen Kera makaman nukilya. Amma ita ko Iran din, a ko yaushe nanata cewa take yi, ta gina kafofin ne don samar wa kanta isasshen makamashi na wutar lantarki, kuma za ta yi amfani da kafofin ne ta hannuka mai sanda.

Su dai Kasashen Turai da Amirka, sun dage kan cewa, idan al’amura suka tabarbare, aka gaza shawo kan Iran, to za su sanya mata jeri ne na takunkumai.

Jumhuriyar Islaman ta Iran dai, ta yanke shawarar katse duk wasu huldodi da hukumar IAEA din ne, don mai da martani ga shawarar da kwamitin mashawartanta ya yanke a ran asabar da ta wuce ta kai Kararta gaban kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya.