1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran ta samu sabon shugaba

Hauwa Abubakar AjejeAugust 3, 2005

An nada Ahmedinajad a matasyin shugaban kasar Iran,cikin kiraye kiraye na dakatar da sarrafa nukiliya

https://p.dw.com/p/Bvae

Shugaban addini na Iran Ayatollah Ali Khameni a yau ya tabbatar da Ahmedinajad dan shekaru 49 da haihuwa dan raayin mazan jiya kuma tsohon dan gwagwarmaya a lokacin juyin juya hali na Iran,a matsayin shugaban kasar ta Iran bayan lashe zabe da yayi a watan yuni da ya gabata.

A jawabinsa na farko sabon shugaban na Iran ya bukaci a kawo karshen da a kawo karshen yaduwar makaman kare dangi a duniya baki daya,kwana daya bayan kasashen yammamcin duniya sun aike da kakkarfar kashedi ga Tehran akan barazanar da tayi na komawa aiyukanta na nuclear.

Cikin ihu na Allah ya halaka Amurka,Allah ya halaka Israila daga jamian Gwamnati da suka halarci bikin tabbatar da Ahmedi a matasayin shugaban kasar,Khameni yayi kira ga Ahmedinajad da kada yayi watsi da yancin kasar,na tattalin arziki da siyasa,ya ce dole ne su kare martabar kasarsu.

Ahmedinajad cikin jawabin nasa yayi alkawarin ganin an tabbatar da adalci a duniya,a cewarsa duniyar yanzu tana bukatar a tabbatar da adalci a koina,ya jaddada cewa a matasayinsa na bawan jamaar Iran zai yi iyaka kokarinsa na ganin cewa yak are mutuncin yan kasar da kuma addinin musulunci

Ya kuma yi alkawarin maida hankali akan marasa galihu a kasar,yayinda kuma ya sake nanata mubayaarsa ga wanda ya kirkiro da daular musulunci ta Iran Ayatolla Ruhulla Khomeni da wadanda suka yi shahada a lokacin gwagwarmaya a lokacin yakin juyin juya hali.

Ahmedinajad wanda abokan dawarsa suka kira da mai tastsauran raayin islama kafin ya lashe zaben,ya sha alwashin cewa gwamanatinsa ba zata bada kai ga masu tastsauran raayi ba a kasar.

Ya kuma yi alkawarin cewa zai mika hannun kawance ga kasashen duniya,amma ya fayyace a fili cewa sai kasar da bata nuna kiyayya ga Iran ba.

Amma jamian diplomasiyya dad a masu kare yancin bil adama suna shakkar cewa da kyar Ahmedinajad zai sasanta da kasashen yammaci fiye da yadda tsohuwar gwamanti ta Khatami tayi,a inda yayi ta samun suka daga masu raayin mazan jiya.

Duk wata bukata ko tunanin cewa mai yiwu ne a samu sasantawa ko kulla kawance da Amurka, Ahmedinajad yayi watsi da shi a yayinda ya baiyana cewa kasar Iran tana da karfin da zata rayu ba tare da kawance da Amurka ba, yayinda a nata bangare Amurkan ta zargi Ahmedinajad da laifin sace jamianta a afishin jakadancinta dake Tehran a 1976.

Ahmedinajad ya dai lashe zaben watan Yuni ne da kashi 61.69 cikin dari inda ya kada Khatami,saboda tabbatarwa yan kasar cewa shi musulmi ne na kwarai wanda ya damu da jin dadin rayuwar talakawa.