Iran ta sake nanata cewa ba zata dakatar da shirinta na nukiliya ba | Labarai | DW | 27.02.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Iran ta sake nanata cewa ba zata dakatar da shirinta na nukiliya ba

Kasar Iran ta sake nanata cewa ba zata taba dakatar da shirinta na inganta sinadaren uraniyum ba kwana guda bayanda komitin sulhu yayi ganawar gaggawa game da kin amincewar nata.

Ministan harkokin wajen Iran Manouchar Muttaki yace Iran ba zata sake dakatar da wannan shiri nata ba,mataki da Amurka ta bayar a matsayin sharadi na tattaunawa da Iran din.

Muttaki ya sanarda manema labarai cewa Iran a shirye take ta tattauna da amma ba tare da an gindaya mata wasu sharudda ba.

Yace Iran tun farko a 2003 da ta dakatar da shirin nata tayi ne bisa manufa mai kyau ta samun maslaha tsakaninta da Faransa da Jamus da kuma Burtaniya game da shirin nata,amma daga bisani ta koma inganta sinadarenta bayan ganin cewa tattaunawar ba zata kai ko ina ba.