1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran ta nemi taka birki ga Saudiyya kan Siriya

Yusuf Bala Nayaya
December 27, 2016

Ministan tsaro a Iran ya fada wa gidan talabijin na RT TV cewa kasar ta Iran na duba yiwuwar tura dakaru zuwa Aleppo.

https://p.dw.com/p/2Uvji
General Hossein Dehqan
Ministan tsaron Iran Hossein DehganHoto: CC-BY-Wikipedia/Mohammad Hasanzadeh

An bukaci taka birki ga mahukuntan Saudiyya dan kada su shiga tattaunawa kan shirin zaman lafiya a Siriya. Ministan harkokin tsaro na kasar Iran Hossein Dehghan ya bayyana haka a zantawa da gidan talabijin na RT TV da ke samun goyon bayan mahukuntan Rasha kamar yadda kamfanin dillancin labarai na RIA ya bayyana a ranar Talatan nan.

An dai jiyo ministan na fadin cewa idan har ana so Shugaba Bashar al-Assad ya sauka daga mulkin kasar wannan na nufin mahukuntan na birnin Riyadh kada su shiga tattaunawar zaman lafiya da za a yi a kan kasar ta Siriya nan gaba.

Har ila yau ministan Dehghan ya fada wa gidan talabijin din na RT TV cewa kasar ta Iran na duba yiwuwar tura dakaru masu bada shawara zuwa birnin Aleppo  idan har bukatar hakan ta taso.