1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran ta musanta hari kan sojojinta a Siriya

Abdul-raheem Hassan
April 30, 2018

Wani harin makamin roka a sansanin sojoji a tsakiyar Siriya ya kashe mutane 26, kungiyar kare fararen hula ta Syrian Observatory for human right ta ce harin ya jikkata mutane 60.

https://p.dw.com/p/2wvep
Syrien Schiitische Gruppen
Hoto: picture-alliance/AP Photo/J.al-Helo

Rahotani da ke fitowa daga kudancin lardin Hama a Siriya, na cewa yawancin wadanda harin ya ritsa da su 'yan kasar Iran ne da ke zaune a sansanin sojojin kasar. Sai dai sanarwar kungiyar kare fararen hulan Siriyan ta ce sojojin Siriya hudu na cikin wadanda harin ya ritsa da su.

Hukumomin birnin Damascus sun tabbatar da harin da aka kai da manyan makamai a sansanin sojojin kasar, sai dai ba a bayyana wadan da ke da hannu a harin ba. Amma Iran ta musanta ikirarin kai hari kan sojojinta da ke Siriya.