1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran ta mayar da martani ga kasashen yamma

January 11, 2006
https://p.dw.com/p/BvCj

Shugaban kasar Iran, Mahmud Ahmadinejad yayi watsi da sukar da kasashen yamma suka yiwa kasar sa, game da matakin ta na ci gaba da gudanar da bincike a daya daga cikin tashohin nukilir ta.

Mahmud Ahmadinajed, wanda ya fadi hakan a wani jawabi daya gabatar ta kafafen yada labarun kasar a yau din nan , yaci gaba da cewa babu gudu babu ja da baya game da wannan shiri da kasar ta Iran ta dauka, duk kuwa da barazanar da ake mata na kaka ba mata takunkumi.

Wannan dai bayani na Ahmadinajed yazo ne jim kadan bayan faraministan Biritaniya, Tony Blair yace zai ja gaban gurfanar da kasar ta Iran a gaban kwamitin sulhu na Mdd don ladaftar da ita.

Mr Blair wanda ya fadi hakan a gaban majalisar dokokin kasar, ya tabbatar da cewa ba zai gajiya ba wajen ganin kasar ta Iran ta martaba dokokin Mdd.

Rahotanni dai sun nunar da cewa, a gobe alhamis ne ministocin harkokin wajen Jamus da Faransa da kuma Biritaniya zasu gudanar da wani taron koli a birnin Berlin na Jamus, don sanin matakin daya kamata su dauka a game da wannan mataki na Iran din.