Iran ta lashi takobin cigaba da shirin ta na Nukiliya | Labarai | DW | 06.03.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Iran ta lashi takobin cigaba da shirin ta na Nukiliya

A yau hukumar makamashin Nukiliya ta majalisar dinkin duniya ke gudanar da taro domin zartar da hukunci na gabatar da kasar Iran a gaban kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya. Shugaban hukumar makamashin nukiliyar, Mohammed El Baradei zai gabatar da rahoton sa ga kwamitin gudanarwa wanda ke da wakilaci na kasashe 35. Babban jamiín kasar Iran a kann shirin makamashin nukiliyar Ali larijani yace Iran zata ci gaba da sarrafa sinadarin ta na Uranium idan aka gabatar da ita ga kwamitin tsaron na majalisar dinkin duniya. Jakadan Amurka a majalisar dinkin duniyar John Bolton ya gargadi da cewa Iran zata dandana kudar ta idan ta cigaba da aiwatar da shirin makamashin nukiliyar. Sai dai kuma a hannu guda kasashen China da Rasha basa goyon bayan daukar matakan kakabawa kasar Iran din takunkumi. Amurka da kasashen tarayyar turai na zargin Iran da yunkurin mallakar makamin kare dangi. A nata bangaren Iran ta ce makamashin ta na lumana ne domin samar da hasken wutar lantarki ga alúmar ta.