Iran ta kori Jami′in Diplomasiyyan Jamus | Labarai | DW | 05.01.2008
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Iran ta kori Jami'in Diplomasiyyan Jamus

An tilastawa jami'in Diplomasiyya na kasar Jamus barin Iran.Ana dai rade radin cewar hakan bazai kasa nasaba da martanin,koran jamiin kasar ta Iran da akayi daga nan tarayyar Jamus ba.Mujallar Der Spiegel dake nan jamus ta ruwaito a watan Disamban daya gabata cewar,hukumomin kasar sun kori wani jamiin diplomasiyya na kasar Iran ,adangane da zarginsa da kokarin sayen wasu naurori domin harkokin makamashin Nuclear da kasar ke fuskantar adawa dashi.Maaikatar harkokin wajen jamus din dai ta tabbatar dacewar jamiin diplomasiyyan ta yabar kasar ta Iran,sai dai babu bayanai dangane da dalilin da yasa hukumomin Iran din suka kore shi.