Iran ta koma ga aikin binciken fasahar nukiliya | Labarai | DW | 10.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Iran ta koma ga aikin binciken fasahar nukiliya

A cikin wata sanarwa da ta bayar Iran ta ce cibiyoyin binciken nukiliya a cikin kasar sun fara aiki. Da farko hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa ta tabbatar da cewar Iran ta bude tashoshin nukiliyarta da hukumar ta rufe. Duk da korafe korafen da kasashen duniya ke yi, a cikin makon jiya gwamnati a birnin Teheran ta ce zata fara binciken fasahar narka karafan nukiliya wanda ake amfani da su wajen samar da sinadarin uranium. Ministan harkokin wajen Jamus Frank-Walter Steinmeier ya ce matakin da Iran ta dauka ya sabawa yarjejeniyar da ta kulla da KTT a birnin Paris. Amirka wadda ke zargin Iran da kokarin kera makaman nukiliya a boye, ta ce za´a yi karar gwamnatin Teheran a gaban kwamitin sulhun MDD.