Iran ta ki mika wuya. | Siyasa | DW | 31.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Iran ta ki mika wuya.

Har ila yau dai Iran na nan kan bakanta na kin mika wuya ga sharuddan da kasashen Yamma ke gindaya mata game da btun shirinta na fasalta sinadarin ureniyum.

Shugaba Ahmadinijad na kasar Iran.

Shugaba Ahmadinijad na kasar Iran.

Ita dai Iran, har ila yau ba ta nuna wata damuwa ba ga shawarar ba zato ba tsammanin da kasashen Yamma da kuma Rasha da Sin, suka yanke game da kai kararta gaban kwamitin sulhu na Majalisar dinkin Duniya, game da kin da ta yi na mika wuya ga kiran da a galibi kasashen Yamman ke yi mata na ta soke shirye-shiryenta na mallakar cibiyoyin sarrafa makamashin nukiliya.

Da yake amsa tambayoyin maneman labarai game da wannan hukuncin, shugaban Hukumar Makashin Nukiliyan ta kasar Iran Aghazadeh, ya bayyana cewa, babu wata dokar da ke hujjanta kai karar kasarsa gaban kwamitin sulhun. Su ma kafofin yada labaran kasar ta Jumhuriyar Islama, ba su ba da wani muhimmanci ga daidaiton da kasashen Yamman suka cim ma da Rasha da Sin ba. Sun fi mai da hanakalinsu ne kan bukukuwan ibada na watan Muharram da mabiya darikar sh’iti ke yi, wadanda kuma za a fara yau talata din nan. A gefen duk shirye-shiryen gidan talabijin din kasar ne aka ambaci batun makamashin nukiliyan.

Ko da Iran din ta damu da yarjewar da kasashen Yamma suka yi da Sin da Rasha ma, ba ta nuna hakan a bayyane ba. Halin da take nunawa a yanzu ne dai na kin ja da baya daga manufar da ta sanya a gaba. Kamar yadda mukaddashin shugaban kwamitin tsaro na kasar, Javad Vaiidi ya bayyanar:-

„Ba za mu taßa ja da baya ba, daga hakkin da al’umman Iran ke da shi na gudanad da bincike da kuma inganta shirye-shiryenmu na makamshin nukiliya.“

Hakan dai na tabbatad da cewa, Iran ba za ta saduda ba. Sai dai a halin yanzu, tana nuna sassauci ne ga mai da martani da kalamomi masu kaifi. A kwanaki kadan da suka wuce dai, mahukuntan kasar sun yi barazanar korar jami’an Hukumar Makamashin Nukiliya ta kasa da kasa da ke sa ido a kan ayyukan inganta darajar sinadarin ureniyum ne a cibiyoyin makamahinta, idan aka kai wannan batun gaban kwamitin sulhun a birnin New York.

Ali Larijani, shugaban kwamitin tsaro na kasar Iran baki daya, ya jißinta kai karar kasarsa gaban kwamitin sulhun ne da katse duk wasu hanyoyin diplomasiyya na sasanta rikicin. Amma mukaddshinsa Vaiidi, cewa ya yi:-

„Muna dai bai wa hukumar IAEA hadin kai. Kuma nan gaba ma, kamar dai yadda muka saba a da, za mu karfafa aikin hadin gwiwarmu ne da jami’an binciken tashoshin nukiliyan na kasa da kasa, bida ka’idodjin kasa da kasa da aka yarje a kansu.“

Iran din dai har ila yau, na nanata cewa, tana da sha’awar ci gaba da tattaunawa da da kungiyar Hadin Kan Turai, amma ba har innanaha ba. A ganin mahukuntan birnin Teheran, za a iya warware wannan matsalar ta hanyar diplomasiyya. Sai dai har ila yau, babu wanda ya san inda wannan hanyar ta kantara.