Iran ta kalubalanci kasashen yamma akan aniyar ta | Labarai | DW | 11.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Iran ta kalubalanci kasashen yamma akan aniyar ta

Shugaba Mahmud Ahmadinajad na Iran yace kamfe na batun dakile yaduwar fasahar makamin nukiliya da kasashen yamma keyi, karya ce kawai.

Ahmadinajad, wanda ya fadi hakan a lokacin wata ziyara daya kai Indonesia, yace kasashen dake kalubalantar aniyar kasar Iran na mallakamar makamin na nukiliya, a kullu yaumin sai sunyi gwaje gwajen na su makamin na nukiliya.

Har ilya yau, shugaban na Iran ya shaidar da cewa, kofofin kasar a bude suke na tattauna batun nukiliyar kasar ga ko wace kasa a duniya face kasar Israela.

A waje daya kuma , shugaban kasar na Indonesia, Susilo Bambang Yudyuyono, yace hanyar diplomasiyya itace hanya daya da zata taimaka wajen warware takaddamar rikicin nukiliyar kasar ta Iran.

Bisa hakan yace, kasar sa a shirye take ta taimaka wajen ganin an warware wannan rikici ta hanyar ruwan sanyi