Iran ta fara nuna sassauci akan kalaman nuna kyamar Isra´ila | Labarai | DW | 29.10.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Iran ta fara nuna sassauci akan kalaman nuna kyamar Isra´ila

Tare da sara tana duban bakin gatari Iran ta fara sassautowa daga kalaman da shugabanta Mahmud Ahmedi Nejad yayi na a shafe Isra´ila daga taswirar duniya. A cikin wata sanarwa da ta bayar ma´aikatar harkokin waje ta ce gwamnatin birnin Teheran na biyayya da kudurorin MDD kuma ba zata taba yin amfani da karfi akan wata kasa ba. Shugaba Ahmedi Nejad dai sha suka da kakkausar lafazi daga kasashen duniya bayan da yaki janye furucin da yayi na kyamar Isra´ila. A jiya kwamitin sulhu na MDD ya fitar da wata sanarwa wadda ta soki lamirin shugaban na Iran. A wani taron gangamin kin jinin Isra´ila da ya halarta jiya juma´a a birnin Teheran shugaba Ahmedi Nejad ya dage akan kalaman da yayi.