1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran ta fara ɗura makamashi a tashar Nukiliyarta dake Bushehr.

August 21, 2010

Tashar Nukiliyar Iran ta Bushehr ta fara aiki shekaru 35 bayan fara aikinta.

https://p.dw.com/p/OtFV
Tashar Nukiliyar Iran a BushehrHoto: AP

Hukumomin Iran dana Rasha sun ƙaddamar da buɗe tashar makamashin Nukiliyar Iran dake kudancin birnin Bushehr kusan shekaru 35 bayan fara aikin gina tashar. Hukumar makamashin Nukiliya ta ƙasar Rasha Rosatom wadda aka baiwa aikin gina tashar da kuma samar da sunduƙin makamashin za ta ɗebe tiƙar sinadaran da aka gama amfani da su domin kaucewa sake amfani da su ta hanyar da bata kamata ba. Hukumar Majalisar Ɗinkin Duniya mai lura da hana yaɗuwar makaman Nukiliya za ta sa ido tare da bi sau da ƙafa ayyukan cibiyar domin tabbatar da cewa bata saɓa ka'ida ba.

Nan da watan Nuwamba ne ake sa ran murhun makamashin Nukiliyar zai fara samar da wutar lantarki ga cibiyar bada wutar lantarkin ta ƙasa. Ƙasashen yammacin turai ba su tsananta sa ido akan tashar makamashin ta Bushehr kamar sauran cibiyoyin Nukiliyar Iran ba, kasancewar ƙasashe da dama na ƙetare na da hannu a aikin  gudanar da shi. Da ya ke jawabi game ga manema labarai shugaban tashar makamashin Nukiliyar Iran Ali Akbar Salihi ya yi bayani yana mai cewa " Manufarmu ita ce mu nunawa ƙasashen duniya cewa muna da iko da fasahar da zamu iya samarwa kanmu makamashi ko da wani abu zai taso ɓakatatan.

Mawallafi : Abdullahi Tanko Bala Edita Zainab Mohammed Abubakar