1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran ta fadada shirinta na inganta Uranium

October 28, 2006
https://p.dw.com/p/BueB
Kamfanin dillancin labaru na daliban kasar Iran, ISNA ya rawaito cewa kasar ta fara inganta sinadarin uranium a wani mataki na biyu na gwajin karfin karafan makamashin nukiliya. Kamfanin na ISNA ya ce hakan na nufin an fadada shirin na nukiliya wanda kasashen yamma ke nuna fargabar cewa na kera makaman nukiliya ne. A dangane da haka shugaban Amirka GWB ya ce dole gamaiyar kasa da kasa ta karfafa kokarin da take yi na hana Iran samun fasahar nukiliya. To amma ministan tsaron Rasha Sergei Ivanov ya ce ka da a yi riga malama masallaci da cewa Iran na da fasahar samar da ingantaccen sinadarin uranium wanda za´a iya kera makamin nukiliya da shi. Saboda haka shi fa bai ga wani abin damuwa a nan ba.