1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran ta dage kan bakanta, na ci gaba da aiwatad da shirye-shiryen makamashin nukliyanta.

August 31, 2006
https://p.dw.com/p/Buky

Yau ne ranar cikar wa’adin da kwamitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya ya bai wa Iran da ta dakatad da ayyukan sarrafa sinadarin yureniyum da take yi, in ko ba haka ba ta huskanci takunkumin da za a sanya mata. Amma sa’o’i kaɗan kafin cikar wa’adin, shugaba Mahmoud Ahamdinejad na ƙasar Jumhuriyar Islaman, ya ce Iran ba za ta miƙa wuya ga masu angaza mata ta soke shirye-shiryenta na mallakar makamashin nukiliyan ba. Mahukuntan birnin Teheran dai sun dage ne kan cewar, ba za su dakatad da manufarsu ba, tun da shirin sarrafa sinadarin yureniyum ɗin na hannunka mai sanda ne, kuma ƙasar na da hakkin gudanad da wannan aikin.

A halin da ake ciki dai, ministan harkokin wajen Jamus Frank-Walter Steinmeier, ya sake bayyana shakkunsa ga ikirarin da Iran ke yi na cewa ba ta da niyyar ƙera makaman ƙare dangi. Ya kuma ce asashen Larabawa ma na nuna damuwarsu game da manufofin da Iran ɗin ta sanya a gaba.

Wasu rahotanni dai sun ce Jamus da wasu ƙasashen Yamma na tattauna wani shiri da ya ƙunshi matakai guda uku na sanya wa Iran ɗin takunkumi.