Iran ta da da yiwa kasashen yamma gargadi | Labarai | DW | 19.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Iran ta da da yiwa kasashen yamma gargadi

Kasar Iran ta da da yiwa kasashen yamma gargadin cewa saka mata takunkumi, abu ne da ba ita kadai zai shafa ba, domin hakan a cewar ta ka iya kawo hauhawar farashin man fetur a duniya.

Bayanin daya fito daga bakin ministan ma´aikatar man kasar wato Davoud Danesh Jafari, yazo ne a dai dai lokacin da kasashen yamma da kasar Amurka ke tunanin gurfanar da kasar ta Iran a gaban Mdd don sakala mata takunkumi.

Tunanin daukar wannan matakin daga bangaren kasashen masu fada aji a duniya, ya biyo bayan hasashen da suke yine na cewa kasar ta Iran na kokarin kera makamin nukiliya, wanda hakan ke a matsayin barazana ga zaman lafiyar duniya.

Tuni dai mahukuntan na Iran suka ce nukiliyar da suke kokarin kerawa ta zaman lafiya ce , amma ba ta tashin hankali ba.