1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran ta ce za ta ci gaba da harkokinta na makamashin nukiliya duk da barazanar da kasashen yamma ke yi mata.

January 12, 2006
https://p.dw.com/p/BvCe

Iran ta ba da sanarwar cewa, za ta ci gaba da ayyukan bincike kan makamashin nukilyanta duk da barazanar da gamayyar kasa da kasa ke yi mata ta kai kararta gaban kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya. Tun ran talatar da ta wuce ne jami’an kasar suka fara aiki kan shirye-shiryen makamshin nukiliyanta, abin da ya kawo karshen dakatad da shirin karkashin wata yarjejeniyar da aka cim ma da Jamus da Faransa da kuma Birtaniya a cikin watan Nuwamban shekara ta 2004. Rahotanni dai sun ce ministocin harkokin wajen kasashen EUn guda 3 za su yi wani taro a birnin Berlin nan ba da dadewa ba, don yanke shawara kan dakatad da tattaunawar da ake yi da Iran. Tun fiye da shekar biyu ke nan dai da kasashen Birtaniyan da Faransa da Jamus ke ta kokarin samo bakin zaren warware rikici kan batun makamshin nukiliyan da Iran, amma ba tare da cim ma wata nasara ba.