1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran ta ce da sake a game da makamashin nukiliya

March 12, 2006
https://p.dw.com/p/Bv5G

Gwamnatin kasar Iran ta sanar da kin amincewa da shawarar kasar Rasha na kawo karshen sa toka sa katsi a game da shirin ta na makamashin nukiliya. Fadar Mosco ta bada shawarar sarrawa Iran makamashin na Uranium a kasar Rasha domin kawar da shakku da ake cewa Iran na shirin mallakar makamamin kare dangi. Kakakin maáikatar harkokin wajen Iran Hamid Reza Asefi yace Iran ba ta shirin yin watsi da ikon ta na sarrafa makamashin na Uranium na lumana. Hukumomin kasar Rasha sun ce zasu yi nazarin wannan matayi da Iran din ta dauka. A bangare guda kuma shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yi kira da a samo hanyoyi na diplomasiyya domin sulhunta rikicin nukiliyar ta Iran. Angela Merkel ta baiyana hakan ne a yayin wata ganawa da shugaban kasar Masar Hosni Mubarak a birnin Berlin. Merkel ta ja hankalin kasashen duniya su kaucewa rarrabuwar kawuna da aka fuskanta a baya lokacin da Amurka ta afkawa Iraqi da yaki a shekara ta 2003. Shugaban kasar Iran Mahmoud Ahmedinejad yace Iran na iya saukowa daga matsayin da ta dauka idan har aka yi adalci a sasanta batun nukiliyar.