Iran ta ce ba ta da niyar kaiwa Isra´ila hari | Labarai | DW | 29.10.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Iran ta ce ba ta da niyar kaiwa Isra´ila hari

A yau asabar Iran ta yi kokarin kwantar da hankalin duniya dangane da kalaman da shugaban ta yayi baya-bayan nan na a shafe Isra´ila daga taswirar duniya. Wata sanarwa da ma´aikatar harkokin waje ta bayar ta ce gwamnati a birnin Teheran ba ta da wata niyar afkawa Isra´ila da yaki. Sanarwar ta ci-gaba da cewa har wayau kasar Iran mai bin tsarin Islama na biyayya ga kudurorin MDD kuma ko kadan ba ta taba tunanin amfani da karfi akan wata kasa ko ma yi mata baranaza ba. To sai dai ma´aikatar ta yi fatali da martanin da kwamitin sulhu na MDD ya mayar dangane da kalaman na shugaba Mahmud Ahmedi Nejad ta na mai cewa ba abin karbuwa ba ne. Ma´aikatar harkokin wajen dai ta ce mai yasa kwamitin sulhun bai yi tir da barazanar da Amirka da Isra´ila suka yi ta afkawa Iran ba. A jiya dai ne kwamitin sulhun yayi tir da kalaman kyamar Isra´ila da shugaba Ahmedi Nijad yayi. A cikin wani kuduri da ya zartas, kwamitin sulhu yayi kira ga dukkan kasashe membobin MDD da su guji yin kalamai ko wasu abubuwan masu yin barazana ga ´yancin wanzuwar wata kasa.