1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran ta bukaci a kirkiro sabuwar kasar Israela a nahiyar Turai

December 8, 2005
https://p.dw.com/p/BvHL

Shugaba Ahmadijanad na kasar Iran yace kamata yayi a tashi kasar Israela daga inda take yanzu, wato yankin Gabas ta tsakiya izuwa nahiyar turai.

Shugaban na Iran yaci gaba da cewa matukar tarayyar Jamus da kasar Austria sun amince da kisan kiyashin da suka yiwa bani Yahudu a lokacin yakin duniya na biyu , to kamata yayi a kirkiro musu kasar su daga cikin wadan nan kasashe biyu, ba wai yankin gabas ta tsakiya ba.

Shugaban na iran wanda ya fadi hakan a lokacin yana zantawa da yan jaridu a yau alhamis, ya kwatanta kasar ta Israela tamkar wani kari ne ga duniya.

Game kuwa da wadan nan kalamai na Ahmadinajad din, kakakin ma´aikatar harkokin wajen Israelan wato Mark Ragev , Allah wadai yayi dasu da cewa kalamai ne na kabilanci.

Kakakin ya kara da cewa babu shakka ire iren wadan nan kalamai, abubuwa ne dake nuni da irin gwamnatin da zata kasance a kasar ta iran a nan gaba.

Har ila yau kakakin yaci gaba da cewa ire iren wadan nan kalamai abubuwa ne dake kara tabbatar da cewa , shugaban na Iran ya kaucewa tsari na gamayyar kasa da kasa.

abubuwa ne dake kara tabbatar da cewa, shugaban na Iran ya kaucewar tsari na gamayyar kasa da kasa.

A waje daya kuma ministan harkokin wajen Jamus, wato Frank Walter Steinmeir, shima kakkausar suka yayi da kuma Allah wadai da wadannan kalamai da suka fito daga bakin shugaban kasar na Iran .