Iran ta baje kolin sabbin rokoki masu cin dogon zango | Labarai | DW | 22.09.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Iran ta baje kolin sabbin rokoki masu cin dogon zango

Duk da matsin lamba da kasashen duniya suke mata Iran ta nuna cewa ita wata babbar daula ce. A wajen wani fareti na tunawa da barkewar yakin da ta gwabza da Iraki shekaru 27 da suka wuce, Iran ta nuna wasu sabbin rokokin ta. Kamar yadda kasar ta yi bayani, rokar da ake kira Ghadr ka iya cin zango mai nesan kilomita dubu 1 da 800 wato tana iya kaiwa ga Isra´ila ko wani sansanin Amirka dake yankin Golf. Shugaba Mahmud Ahmedi-Nijad ya sake yin kira ga Amirka da janye daga Iraqi don shafawa kanta da ma yankin baki daya lafiya. Da farko a birnin New York wakilan dindindin na kwamitin sulhun MDD hade da Jamus sun tattauna akan tsananta takunkumai kan Iran a dangane da shirinta na nukiliya.