1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

kasar Iran ta gargadi kasashen Turai

Zulaiha Abubakar
December 8, 2018

Shugaban kasar Hassan Rouhani ya gargadi kasashen Turai kan fuskantar matsalolin Shaye-shaye da kwararrar 'yan cirani da kuma yawaitar hare-haren ta'addanci sakamakon takunkumin da Amirka ta kakabawa kasar.

https://p.dw.com/p/39kI9
Iran Hassan Rohani
Hoto: Getty Images/AFP

Ya kuma kara da cewar matukar takunkumin ya kassara kokarin Iran na magance wadannan matsaloli babu shakka kasashen Turai za su fuskanci kalubale, shi ma da yake tsokaci game da yanayin da kasar Iran din ke ciki ministan harkokin wajen kasar Javad Zarif ya zargi Amirka ta sayar wa da yankin gabas ta tsakiya makaman da suka fi karfin bukatun yankin.