Iran ta baiwa Hamas gudunmawar dala Miliyan 50 | Labarai | DW | 16.04.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Iran ta baiwa Hamas gudunmawar dala Miliyan 50

Gwamnatin ƙasar Iran ta baiyana gudunmawar kuɗi dala miliyan 50 ga hukumar gudanarwar Palasɗinawa, bayan da Amurka da ƙungiyar tarayyar turai suka janye tallafi ga gwamnatin Palasɗinawan ƙarƙashin jagorancin Hamas. Ministan harkokin wajen Iran Manoucher Mottaki shi ne ya sanar da gudunmawar a Tehran, domin taimakawa sabuwar gwamnatin ta Palasɗinawa. Gudunmawar ta zo ne a daidai lokacin da Hamas ta mika kokon bara ga ƙasashen musulmi, bayan da ƙasashen larabawa suka kasa cika alƙawuran da suka yi na tallafin kuɗi. ƙasashen Israila da Amurka da ƙungiyar tarayyar turai, sun buƙaci Hamas, wadda suka ɗauka a matsayin ƙungiyar yan taádda, ta ajiye makaman ta, ta kuma amince da ƙasar Israila kafin su bata gudunmawar jin ƙai. To amma jagoran ƙungiyar Hamas Kahaled Mashaal ya jaddada ƙin amincewar su da waɗannan sharuɗa, yana mai cewa gwamnatin su ba za ta amince wa ƙasar Israila ba.