1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran ta bada amsa ga komitin sulhu na Majalisar Dinkin Dunia

August 22, 2006
https://p.dw.com/p/Bulv

Ƙasar Iran ta bada ansa, ga wasiƙar komitin sulhu na Majalisar Dinkin Dunia, wadda ta yi mata umurnin wasti da aniyar ƙera makaman nulkeya.

Shugaban tawagar Iran, a tantanawar da ake kan wannan taƙƙadama Ali Larijani, ya buƙaci tun gobe, laraba, ƙasashen 5 masu kujerun dindindin a komitin sulhu tare Jamus su koma tebrin shawara, da tawagar Iran ,domin ci gaba da tantanawa.

To saidai, Larjini bai hito hili ba, ya bayyana ko Iran, ta amince ko kuma a´a, da tayin da ƙasashen su ka yi mata.

Idan dai ba a manta, komitin sulhu a Majalisar Dinkin Dunia, ya ba Iran ranar 31 ga watan Ogust, a matsayin wa´adin ƙarshe na dakatar da aniyar ta,ta kera makaman nuklea, idan kuma ba haka ba, ta fuskanci dokokin Majalisar Dinkin Dunia,da su ka haɗa da takunkumin karya tattalin arziki.

Jikadan Amurika a Majalisar Dinkin Dunia, John Bolton ya ce Amurika zata yi nazarin wannan amsa, ta kuma maida martani a lokacin da ya dace.