Iran na shirin kiran taro kan kisan kiyashin da aka yiwa Yahudawa | Labarai | DW | 15.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Iran na shirin kiran taro kan kisan kiyashin da aka yiwa Yahudawa

Gwamnatin Iran ta ba da sanarwar cewa ta na shirin kiran wani babban taro don yin nazari a kimiyyance don tabbatar da gaskiyar aukuwar kisan kiyashin da ´yan Nazin Jamus suka yiwa Yahudawa. Kakakin ma´aikatar harkokin waje Hamid Reza Asefi wanda ya ba da wannan sanarwa bai bayyana wuri ko kuma lokacin da za´a yi wannan taro akan kisan kiyashin ba. Hakazalika ba´a sani ba ko shi ma zai halarci wajen taron. A karshen shekarar da ta wuce shugaban Iran Mahmud Ahmedi-Nijad ya bayyana kisan kiyashin da cewa wata almara ce sannan yayi kira da a goge Isra´ila daga doron kasa. Kalaman na sa dai sun sha suka daga ko-ina cikin duniya.