Iran da Saudiyya na kokarin daidaitawa | Labarai | DW | 03.09.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Iran da Saudiyya na kokarin daidaitawa

Ma'aikatar harkokin wajen Iran ta ce nan da 'yan makonni jami'an diflomasiyyar kasar za su ziyarci takwarorinsu na Saudiyya don yin wata tattaunawa da ake tunanin ta dinke baraka ce tsakanin kasashen biyu.

Mai magana da yawun ma'aikatar Bahram Ghassemi ne ya bada tabbacin hakan a wata hira da aka yi da shi dazu, inda ya ke cewar jami'an Iran da na Saudiyya za su ziyarci juna musamman ma ofisoshin jakadancinsu. A kwanakin baya ne Iran ta fara nuna alama ta yin sulhu da Saudiyya din wanda suka shafe kimanin shekaru biyu suna rikici na diflomasiyya biyo bayan afkawa ofishin jakadancin Saudiyya din a Iran bayan da mahukuntan Riyadh suka aiwatar da hukuncin kisa kan shararren malamin shi'ar nan Nimr al-Nimr.