Iran da rikicin Nuclear | Labarai | DW | 30.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Iran da rikicin Nuclear

Shugaba Mahmoud Ahmadinejad na kasar Iran yayi gargadin cewa,Tehran zata mayar da martani adangane da kowane irin takunkumi mdd zata kakaba mata adangane da shirin Nucleanta.Dayake jawabi wa alummomin yankin Pishva dake wannan kasa,Shugaban na Iran yace,kasarsa bata neman tashin hankali ,amma dukkan wani yunkuri na tozarta mata ,zai samu martani daga jamaar kasar.Tuni dai jamian kasar ta Iran suka lashi takobin mayar da martani,adangane da kowane irin takunkumi aka kakabawa kasar,sai dai sunce zaa san irin martanin da zasu mayar kadai,bayan an dauki matakan ladabtarwa akan Tehran.