1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran da Rasha sun cimma yarjejeniya ta farko

February 26, 2006
https://p.dw.com/p/Bv6f

Iran da Rasha sun amince da yarjejeniya ta farko akan shirinta nukiliya da ake ganin na makaman kare dangi ne.

Da suke magana wajen taron manema labarai na hadin gwiwa shugaban hukumar makamashin nukiliya na Rasha Sergei Kiriyneko da mataimakin shugaban kasar Iran Gholam Reza Aghazadeh,sunce zasu ci gaba da tattaunawa a cikin kwanakin nan.

Mataimakin shugaban kasar ta Iran yace sun amince kafa kanfanin hadin gwiwa na sarrafa makamashin nukiliya.

Kasar Rasha wadda take da ikon darewa kujerar naki a komitin sulhu na MDD,tana neman shiga tsakani cikin wannan rikici na shirin nukiliya na Iran,wanda kasashen yammacin duniya suke ganin wani shiri ne na samun makaman kare dangi.

Taron na ranar 6 ga watan maris zai yanke shawara akan matakin daya kamata komitin sulhu zai dauka domin ladabtar da kasar Iran.