Iran da Komitin Sulhu | Labarai | DW | 09.03.2006
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Labarai

Iran da Komitin Sulhu

A farkon makon gobe nedai ake saran komitin Sunhun majalisar dunkin duniya zatayi mahawara a dangane da rikicin nuclearn Iran .Wannan ya biyo bayan kada kuriu ne da hukumar kula da Nuclear ta kada,adangane da gabatar da Tehran gaban Komitin,wanda kuma zai iya jagorantar kakaba mata takunkumi.Ana dai saran cewa wakilan komitin sulhun 15,zasu gabatar da kudurinsu akan harkokin Nuclean kasar ta Iran.To sai dai ya zuwa yanzu kasashe masu zaunannen kujera a komitin da suka hadar da Amurka,da Rasha da Sin da Faransa da Britania,basu cimma yarjejeniya kann wannan kuduri ba.Ministan harkokin wajen Jamus Frank-Walter Steinmeire ya bukaci da abi hanyar diplomasiyya wajen warware rikicin Nuclearn na Iran.A yau madai Iran din ta sanar dacewa kofar ta bude yake domin tattaunawa,sai dai taki amincewa dakatar da sarrafa sinadaran Uranium dinta.

 • Kwanan wata 09.03.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammed
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu7X
 • Kwanan wata 09.03.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammed
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu7X