Iran da Jordan sun yi lalle marhabin da yarjejeniya tsakanin yan schi´a da yan sunnin Irak | Labarai | DW | 22.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Iran da Jordan sun yi lalle marhabin da yarjejeniya tsakanin yan schi´a da yan sunnin Irak

Ƙasashen Iran da Jordan, sun yi lalle marhabin da yarjejeniyar zaman lahia, da aka rattaba hannu kan ta, tsakanin yan schi´a, da yan sunnar Irak, a ƙasar Saudi Arabia.

Kakakin ministan harakokin wajen Iran, Mohamed Ali Hossaini, ya yi kira ga ɓangarorin 2, su mutunta wannan yarjejeniya, ya kuma bukaci gwamnatin Irak, ta yi belin pirsinonin da ke cikin hannun ta.

Saidai kwana ɗaya rak, bayan cimma sulhun, babu alamun, samun kwanciyar hankali a Irak.

A yau ma, yan ƙunar baƙin wake, sun kai hare- haren- da su ka yi sanadiyar mutuwar mutane 6.

Sannan, rundunar Amurika, ta bayyana mutuwar sojin ta, ɗaya a filin daga.

Tun daga mamayar Irak, watan Ramadan na wannan shekara, ya hi zama mafi muni, ga Amurika, a sakamakon assara sojoji kussan 80 da ta yi, a wannan ƙasa.