1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran da Amirka sun yaba yarjejeniyar da aka cimma

Salissou BoukariJuly 14, 2015

Shugaban Jamhuriyar Muslunci ta Iran Hassan Rohani ya bayyana gamsuwarsa dangane da yarjejeniyar da aka cimma kan batun nukiliyar kasar ta Iran.

https://p.dw.com/p/1FyOE
Iran Staatspräsident Hassan Rohani
Hoto: http://www.president.ir

Cikin wani jawabi da ya yi ta kafofin yada labarai na kasar, Shugaban na Iran Hassan Rohani ya ce Allah ne ya ji rokon al'ummar kasar ta Iran da ya bada dama aka kai ga wannan mataki. A nashi jawabin Shugaban Amirka Barack Obama, ya ce wannan yarjejeniya da aka cimma tsakanin kasar ta Iran da sauran manyan kasashen yamma, za ta bada damar buda wani sabon babi na hulda tsakanin Amirka da kasar ta Iran, inda ya yi alkawarin yaye takunkumin da aka kakaba wa kasar ta Iran. Sai dai Obama ya ce idan kuma Iran din ta saba alkawari to za'a mayar mata da takunkuminta.

Sai dai yayin da manyan kasashe kamar su Ingila da Faransa ke yaba wannan yarjejeniya, daga nata bengare kasar Saudiya nuna dari-dari ta yi kan lamarin, inda ta ce hakan na da kyau idan har kasar ta Iran bazata dagula lissafin kasashen gabas ta tsakiya ba.