Iran: Amirka ta daina barazana wa Koriya ta Arewa | Labarai | DW | 06.09.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Iran: Amirka ta daina barazana wa Koriya ta Arewa

Shugaban kasar Iran Hassan Rohani ya ce bazanar da Amirka ke yi wa Koriya ta Arewa ce ta sanyata yin gwajin makamin nukiliya, inda ya ce kuma wannan wani wasa ne mai hadarin gaske ga duniya baki daya.

Hassan Rohani (Irna)

Shugaban kasar Iran Hassan Rohani

 

Shugaban kasar ta Iran ya ce akwai wani da ta kamata ya yi wasa idan ana batun makamin nukiliya? Don haka idan kasa ta mallaki irin wadannan makamai duk wani garaje na yi ma ta barazana na a matsayin mugun wasa mai cike da hadari ga duniya baki daya.

A Ranar lahadi ce dai Koriya ta Arewa ta aiwatar da gwajinta na shida na makamin nukiliya wanda kuma shi ne mafi karfi daga cikin dukanin gwajin da ta yi a baya. A baya dai shugaban Amirka ya yi wa shugaban na Koriya ta Arewa Kim Jong-Un barazanar daukan matakin soja mai karin gaske.