1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iraki:An dakatar da Zaben raba gardama na Kurdawa

Gazali Abdou Tasawa
September 18, 2017

Wata babbar kotu Iraki ta ba da umurni dakatar da yin kuri'ar raba gardama a game da yancin gashin kai na yankin Kurdawa wanda da farko aka shirya yin zaben a ranar 25 ga wannan wata.

https://p.dw.com/p/2kCXq
Irak Erbil - Parlamentssitzung zum Unabgängigskeitsreferendum
Hoto: Reuters/A. Lashkari

Wata sanarwa gwamnatin ta Iraki ta ce an dakatar da zaben ne har sai an bincike wasu korafe-korefen da aka shigar a game da zaben wanda wasu ke cewar ya sabama kaidar kudin tsarin mulkin. Wasu majiyoyin sun ce 'yan majalisu akalla guda takwas ne na 'yan Shi'a da Turkumenes wasu tsirarun kabilun da ke a arewacin Bagadaza suka shigar da karan a game da zaben wanda suka ce ya sabama doka.