1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Iraki zata taimawakaTurkiya korar yan tawaye

Ministan harkokin wajen kasar Iraki Hoshyar Zebari ya baiwa takawaransa na Bagadaza tabbacin goyon bayan kasarsa wajen korar Qurdawa yan tawaye a arewacin Iraki.Wajen taronsu da manema labarai da Zebari ministan harkokin wajen Turkiya Ali Babacan ya nanata fatar gwamnatinsa ta magance rikicin ta hanyar siyasa da diplomasiya.Babacan ya kuma ki amincewa da batun tsagaita bude wuta yana mai cewa Turkiya bata son sadaukar da dangantakun aladu da tattalin arziki tsakaninta da Iraki akan batun yan taadda ba.