1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iraki ta kai wa jagororin IS hari a Siriya

Zulaiha Abubakar
May 25, 2018

Kasar Iraki ta sanar da kai hari a sansanin jagororin kungiyar ta'addanci ta IS da ke yankin Hajin a kasar Siriya a ci gaba da ganin an kawo karshen ayyukan ta'addanci gaba daya.

https://p.dw.com/p/2yKUw
Syrien IS-Kämpfer
Hoto: picture-alliance/Balkis Press

Wannan dai shi ne karo na uku da Iraki ke kai hari yankin Hajin wanda ya kasance yanki daya tilo da yayi saura a hannun mayakan na IS. Wani rahoto da cibiyar da ke kula da kare hakkin 'dan Adam ta Birtaniya ta fitar ya bayyana cewar akalla manyan shugabannin kungiyar ta IS  sittin da biyar ne ke zaune a yankin na Hajin wanda ke gabashin kasar ta Siriya.

Sojojin hadin gwuiwa na kasar Siriya da wasu mayakan Kurdawa da dakarun kasashen Larabawa wadanda Amirka ke mara wa baya ne ke zagaye da yankin tun shekara ta 2017.