1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iraki na fuskantar hadarin fadawa cikin mummunan yakin basasa

September 19, 2006
https://p.dw.com/p/Buj2
Babban sakataren MDD Kofi Annan ya sake yin gargadin cewa Iraqi na cikin mummunan hadarin fadawa cikin wani yakin basasa. A lokacin da yake magana a birnin New York Annan ya ce idan aka ci-gaba da tashe tashen hankula a kasar to akwai barazanar rugujewar kasar ta Iraqi. Babban sakataren na MDD ya yi kira ga gamaiyar kasa da kasa da ta tsara wani gagarumin shiri na tsawon shekaru 5 don sake gina Iraqin wadda yaki ya daidaita. Wannan gargadin ya zo ne bayan mutane sama da 40 sun raasa aryukansu a fadin kasar ta Iraqi a jerin hare haren bama-bamai. Mutum 22 suka rasu a birnin Tal Afar dake arewacin Iraqin lokacin da wani dan kunar bakin wake ya ta da bam a cikin wata kasuwa a jiya litinin. Sannan a Ramadi dake yamma da Bagadaza mutum 13 sun mutu a wani harin kunar bakin wake da aka kai a wajen wani wurin daukar ´yan sanda aiki. Yayin da mutum 8 suka kwanta dama sakamakon harbe harbe a birnin Baquba.