Iraki na dab da tsunduma cikin yakin basasa-Mubarak | Labarai | DW | 08.04.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Iraki na dab da tsunduma cikin yakin basasa-Mubarak

Shugaba Hosni Mubarak na Masar ya fadawa tashar telebijin ta Al-Arabiyya cewar ko shakka babu yakin basasa na dab da barkewa a Iraqi kuma wannan rikici ka iya bazuwa a ilahirin yankin GTT idan dakarun Amirka suka fice daga Iraqi a wannan lokaci da muke ciki. Ana dab da tsunduma cikin wani yakin basasa kuma idan Amirka ta fice za´a fuskancin mummunan bala´i domin yakin zai rincabe kuma Iran da sauran kasashe zasu tsoma bakin su a ciki wanda haka zai janyo hauhawar aikin ta´addanci a ilahirin yankin GTT, inji shugaba Mubarak.