Iraki: Bam ya kashe mutane a bikin Aure | Labarai | DW | 09.03.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Iraki: Bam ya kashe mutane a bikin Aure

Hukumomi a kasar Iraki na cewa 'yan kunar bakin wake sun hallaka mutane 21 a lokacin da suke shagulgulan jajiberen bikin Aure a yankin Al-Hajaj da ke arewacin birnin Tikrit.

Likitoci da ke karban jinya sun ce akwai mutane 25 da ke fama da munanan raunuka, sai dai kawo yanzu babu wadanda suka dau alhakin kai harin, amma hukomi a kasar sun ce kungiyar IS ta sha kai hare-hare makamancin wannan a kan fararen hula da ma jami'an tsaro.

A yanzu dai dakarun gwamnatin Iraki na fafatawa a yammacin birnin Mosul na ganin sun karbe iko na sauran yankunan da ke karkashin ikon kungiyar ta IS, inda wasu rahotanni ke cewa tuni jagoran kungiyar Abu Bakr al-Baghdadi ya tsere daga birnin.