Iraki a yau | Labarai | DW | 09.03.2006
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Labarai

Iraki a yau

Rahotanni daga kasar Iraki na nuni dacewa akalla mutane 10 suka rasa rayukansu ayayinda wasu suka jikkata,a hare haren boma bomai a birnin Bagadaza kadai,guda kuwa ya hadar da tashin bomb ne daga cikin wata mota da aka tsayar a kofar shiga asibiti.A wannan harin mota dai fararen hula biyu suka rasa rayukansu,kana wasu mutane 13 suka samu raunuka.Ayayin da safiyar yau din ne kuma wasu mutane 6 suka rigamu gidan gaskiya ,ciki harda da karamin yaro ,baya ga mutane 7 da suka jikkata,a fashewar wani bomb kusa da sansanin sojin Iraki dake yammacin birnin .

Bugu da kari an bindige wasu mutane biyu har lahira a kusa da yankin nan dake dauke da gidajen manyan jamian ketare na green zone,kana wasu yansanda 4 sun samu rauni a musayar wuta da sukayi da yan ta kife dake yammacin Bagadazan.

 • Kwanan wata 09.03.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammad
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu7Z
 • Kwanan wata 09.03.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammad
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu7Z